Mu na maraba da kowa a NNPP -- Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce jam'iyar NNPP na maraba da kowa, inda ya ce kofa a buɗe ta ke ga duk mai sha'awar shiga. 

Kwankwaso ya faɗi haka ne yayin da a ke raɗe-raɗin cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, da sauran ƴan jam'iyar APC na shirin sauya sheƙa zuwa NNPP.

Da ya ke zanta wa da Freedom Radio a jiya Talata a Abuja, Kwankwaso ya ce ba zai yi wu a ce dole sai masoya ne za su shiga jam'iyar ba.

A cewar sa, ko waɗanda a ka samu saɓani da su a baya, kuma su ka nuna sha'awar shigo wa jam'iyar, to kofa a buɗe ta ke.

Ya ƙara da cewa ko ma da wacce irin buƙata mutum ya shigo jam'iyar, to za a zauna a ga irin tsare-tsaren da za a yi domin a biya wa kowa hakkin sa.

"Ko ƴan G-7 ma muna maraba da su domin su ma ba sa jin daɗin abubuwan da su ka faru a jihar Kano a shekaru bakwai da su ka wuce.

"In dai dama mu na son NNPP ta girma ta kuma yaɗu, to dole a baiwa kowa damar ya shiga jam'iyar," in ji Kwankwaso.

Comments

Popular posts from this blog

Sallah: NSCDC deploys 3005 operatives in Kano to ensure safety

YPP Vice President candidate in 2019 criticizes Buhari over increasing insecurity

Tinubu holds crucial meeting with Shekarau, as the Senator’s faction takes control of APC machinery in Kano