KSCPC ta kama gurbatacciyar madara
Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa yace sun samu nasarar kama gurbatacciyar madarar ne katan dari da goma sha hudu, tare da wani matashi wanda ya karbe ta bayan da aka shigo da ita daga jihar Lagos.
Madarar wadda wa'adin amfani da ita ya kare kuma ba ta da lambar hukumar tabbatar da ingancin kayayyaki ta kasa NAFDAC, ana zargin cewa an shigo da ita ne don sayarwa da al'ummar jihar Kano.
A don haka rundunar 'Yansandan karkashin jagorancin kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano CP Sama'ila Shu'aibu Dikko ta gayyato hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa domin damka mata madarar da kuma matashin dake tafe da ita don ci gaba da gudanar da bincike.
Da yake karbar madarar a madadin shugaban hukumar Janar Idris Bello Dambazau, jami'i mai kula da ingancin kayayyaki a hukumar Alhaji Bello Alkarya ya tabbatar daukar matakin day a dace, bayan godewa rundunar wajen tabbatar da bada gudunmawar su don inganta lafiyar al’ummar jihar Kano.
Comments
Post a Comment