ICRC ta tallafawa masu bukata ta musamman a Kano
Kungiyar bada agajin farko ta kasa da kasa ICRC ta baiwa masu bukata ta musamman sabbin injina da za su taimaka musu wajen gudanar da sana'o'in su.
Shugaba a ofishin kungiyar dake jihar Kano Mista Armen Harutyunyan ne ya bada injinan ga masu bukata ta musamman din a jihar Kano.
Mista Armen Harutyunyan sun tallafa musu da injinan walda da janareto da injin fenti ne, don inganta rayuwar su da iyalan su baki daya.
Rahotanni na nuni da cewa, kungiyar ICRC ta jima tana bada wannan tallafin a jihar Kano tun shekarar 2016, wanda shirin ya samu gagarumar nasara akan mutanen da suka amfana da tsarin.
Da yake jawabi bayan karbar kayan tallafin a madadin masu bukata ta musamman din, Farfesa Jibril Isa Diso daga sashen ilmi na musamman dake jami'ar Bayero, yace shakka babu matakin zai taimakawa dimbin al'ummar su, kasancewar ba wai iya wadanda suke gudanar da sana'ar bane za su samu kyautatuwar rayuwa.
"Idan masu ruwa da tsaki za su rinka gudanar da irin wannan ayyukan tallafin, za'a wayi gari ba tare da samun mabarata ba.
"Muna kira da sauran kungiyoyi da su kwaikwayi ICRC don samun sakamako mai kyau," Farfesa Jibril Isa Diso.
Ita dai kungiyar ICRC na gudanar da harkokin jin kai da tallafin al'umma a Najeriya tun a shekarar 1988, wanda bayanai ke nuni da cewa ta gudanar da ayyukan tallafin mutanen da hare-haren kabilanci ko addini ya shafa a bangarori daban-daban na kasar.
Umar Idris Shuaibu, Digital Journalist and a Blogger
shuaibuumaridris@gmail.com
Comments
Post a Comment