The State Deputy Governor Nasir Yusuf Gawuna has assured Agriculture students of the state Government readiness and commitment to assistant them in all of their future endeavors. Nasir Yusuf Gawuna who is also the Commissioner of Agriculture and Natural Resource stated this while speaking shortly after receiving award from the Nigerian Association of Agricultural Students, held at the Bayero University Kano. The Deputy Governor who was represented by the Special Assistant on Special Duties, Honourable Tahir Tudun Fulani also said the present Administration of Governor Dr. Abdullahi Umar Ganduje has been off and doing in trying to provide all Agricultural support to the citizens of the State. The Deputy Governor also emphasis the need for the students to continued explored government opportunities on Agriculture and other ways of tapping the available resources so as to become self-defense in the society after their Academic year. Earlier, the President of the Association Co...
Kungiyar bada agajin farko ta kasa da kasa ICRC ta baiwa masu bukata ta musamman sabbin injina da za su taimaka musu wajen gudanar da sana'o'in su. Shugaba a ofishin kungiyar dake jihar Kano Mista Armen Harutyunyan ne ya bada injinan ga masu bukata ta musamman din a jihar Kano. Mista Armen Harutyunyan sun tallafa musu da injinan walda da janareto da injin fenti ne, don inganta rayuwar su da iyalan su baki daya. Rahotanni na nuni da cewa, kungiyar ICRC ta jima tana bada wannan tallafin a jihar Kano tun shekarar 2016, wanda shirin ya samu gagarumar nasara akan mutanen da suka amfana da tsarin. Da yake jawabi bayan karbar kayan tallafin a madadin masu bukata ta musamman din, Farfesa Jibril Isa Diso daga sashen ilmi na musamman dake jami'ar Bayero, yace shakka babu matakin zai taimakawa dimbin al'ummar su, kasancewar ba wai iya wadanda suke gudanar da sana'ar bane za su samu kyautatuwar rayuwa. "Idan masu ruwa da tsaki za su rinka gudanar da irin wannan...
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta mikawa hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa ta jihar Kano (KSCPC), wata gurbatacciyar madata da ta kama wadda aka shigo da ita jihar Kano don yin amfani da ita. Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa yace sun samu nasarar kama gurbatacciyar madarar ne katan dari da goma sha hudu, tare da wani matashi wanda ya karbe ta bayan da aka shigo da ita daga jihar Lagos. Madarar wadda wa'adin amfani da ita ya kare kuma ba ta da lambar hukumar tabbatar da ingancin kayayyaki ta kasa NAFDAC, ana zargin cewa an shigo da ita ne don sayarwa da al'ummar jihar Kano. A don haka rundunar 'Yansandan karkashin jagorancin kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano CP Sama'ila Shu'aibu Dikko ta gayyato hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa domin damka mata madarar da kuma matashin dake tafe da ita don ci gaba da gudanar da bincike. Da yake karbar madarar a madadin shugaban hukumar Janar Idris Bello Dambazau, jami...
Comments
Post a Comment