Hukumar Hisbah zata dauki sabbin ma'aikata 3500 - Ibn Sina

Umar Idris Shuaibu - Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce zata dauki sabbin ma'aikata 3500 a fadin jihar.

Babban kwamandan hukumar ta Hisbah Sheikh Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyanawa 'The Historica Nigeria'.

Ibn Sina yace wannan na zuwa ne bayan sahalewar da hukumar ta samu daga Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a wani mataki na kara inganta ayyukan hukumar ta Hisbah.

Babban kwamandan yace tsarin daukar sabbin ma'aikatan zai baiwa 'yan Hisbah na sa kai da ake kira 'Hisbah Marshal' fifiko, kana daga bi sani sauran mutane su shigo ciki.

"Kaso saba'in cikin dari za su kasance cikin Hisbah Marshal wanda shakka babu mun gamsu da irin kokari da gudunmawa da suke baiwa hukumar Hisbah daga daukar su zuwa yanzu.

"Sai kuma shalkwatar hukumar ta Hisbah cikin tsarin jadawalin za ta dauki mutane dari biyar, sai kananan hukumomi na kwaryar birnin Kano guda takwas za su dauki dari-dari, sai kuma sauran kananan hukumomi da za su dauki hamsin-hamsin kowannen su.

Babban kwamandan hukumar ya kuma ja hankalin al'umma da su kaucewa fadawa komar bata gari wajen karbar kudin sun don sa su cikin tsarin ma'aikatan da hukumar za ta dauka nan ba da dadewa.

"Duk mai son samun wannan dama to ya garzaya karamar hukumar sa, daga nan ne za'a dauka don turo mana sunayen mutane mu tantance", Harun Muhammad Sani Ibn Sina. 

Ita dai hukumar Hisbah ta jihar Kano an samar da ita ne a shekara ta 2003, da nufin inganta tarbiyya da dabbaka shari'ar musulunci a fadin jihar Kano.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Kano indigene appointed as Chief Vet Officer of Nigeria

How ICRC trains and empower disable, Hisbah guards in Kano

Sallah: NSCDC deploys 3005 operatives in Kano to ensure safety