Dan majalisar tarayya na Takai/Sumaila ya bar jam'iyyar APC
Umar Idris Shuaibu - Kano
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Takai da Sumaila, a zauran majalisar kasa Shamsuddeen Bello Dambazau ya sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP.
Hakan ya biyo bayan zaben fidda gwani da jam'iyyar APC mai mulki tayi a jiya.
Shamsuddeen Dambazau wanda dan gidan tsohon Ministan Harkokin cikin gidan kasar nan ne, kuma tsohon shugaban hafsan sojin kasar nan Janar Abdurrahman Bello Dambazau, ya kasance a zauren majalisar kasa ne tun bayan zaben shekara ta 2019.
  
Comments
Post a Comment