2023: Ghali Sule ya fito takarar Gwamnan Kano

Umar Idris Shuaibu - Kano
Shugaban kungiyar tsoffin daliban kwalejojin kimiyya na Kano da Jigawa (KASSOSA), Pharmacist Ghali Sule ya shiga sahun masu neman kujerar Gwamnan Kano karkashin tutar jam'iyyar PRP mai alamar dan mabudi.

Wannan na zuwa ne bayan wani ziyarar gani na musamman da dan takarar Gwamnan ya kai sakatariyar jam'iyyar ta PRP a safiyar ranar Juma'a.

Pharmacist Ghali Sule na cewa hakan ya zama wajibi don ceto jihar Kano da sauran yankunan kasar nan daga halin da ake ciki.

"Gibin da shugabanni suka bari kullum kara girma yake yi, wanda kai tsaye matsalar ke shafar talaka.

"Bangaren ilmi da lafiya da samar da ruwan sha dama aikin gona na bukatar agajin gaggawa, duba da yadda shugabannin da muke da su a yanzu suka yiwa bangaren shakulatin bangaro.

"Wannan kadan kenan cikin muhimman kudurorin mu da muke so zamu aiwatar.

"Kowa na ganin yadda matsalolin matasa ke kara yawaita a jihar nan tamu, wanda hakan ke da alaka ta kai tsaye da tarbiyya da rashin nagartaccen shugabanci, wanda zamu bada gagarunar gudunmawa a wannan bangaren, a cewar dan takarar Gwamnan Kano a tutar jam'iyyar PRP.

Da yake jawabi tun da fari, shugaban jam'iyyar PRP na jihar Kano, Malam Abba Namatazu, ya bayyana gamsuwar sa da manufofin dan takarar Gwamnan Pharmacist Ghali Sule, wanda yace shakka babu irin mutanen da jam'iyyar ke bukata kenan don yin takarar shugabancin al'umma a dukkan matakai.


Namatazu ya kuma yi alkawarin baiwa dan takarar goyon bayan da ya kamata don kaiwa ga gaci.

Pharmacist Ghali Sule kafin yayi ritaya daga aiki, ya kasance Daraktan kula da bangaren magunguna na hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano (HMB), kana kuma babban Daraktan kula da magunguna na ma'aikatar lafiya ta jiha baki daya.

Pharmacist Ghali Sule ya kasance dan gwagwarma wanda ya bada gudunmawa a kwamitoci daban-dabam na hana siyar da magunguna marasa inganci, da gurbatattun kayan abinci.

A yanzu, ya kasance kasance shugaban kungiyar tsoffin daliban kwalejojin kimiyya na jihar Kano da Jigawa, wacce ta hada kungiyoyin daliban kwalejojin kimiyya da suka fito daga wadannan jihohi da ake kira da KASSOSA.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Kano indigene appointed as Chief Vet Officer of Nigeria

FULL LIST: APC inaugurates state chairpersons from 34 state

Rigimar Jam'iyyar APC- Daga Bello Sharada