Rigimar Jam'iyyar APC- Daga Bello Sharada

 


Ranar Asabar  da daddare, Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya kira taro a gidansa na 'yan uwansa gwamnoni a jam'iyyar APC. 

Makasudin taron na fili shi ne, yadda za a fuskanci taron 'convention' na jam'iyyar APC da aka tsara gudanar da shi ranar Asabar 26 ga watan Maris na shekarar da muke ciki ta 2022 a Eagle Square, da ke Abuja. Amma manufar taron ta sirri ita ce yadda za a ci kwalar Mai Mala Buni ya taka masa burki.

Yadda yake a al'ada,  taron kasa na APC shi ne zai fitar da shugabancin APC zababbe da za su tafiyar da ayyukan jam'iyya daga nan har zuwa 2023  kuma har bayanta. An samu fahimta a tsakanin masu ragamar gwamnatocin jihohi na APC guda 22, cewa a cikin mukaman da ake da su guda 56 duk wanda ya rike mukami daga yankin  kudu na kasar nan a zamanin mulkin Adams Oshiomhole, za a yi musanya ne kawai. Ma'ana, shugaban jam'iyya na kasa a baya ya fito daga kudu, yanzu zata zakuda ta koma arewa. A wancan zubin sakataren jam'iyya dan arewa ne, yanzu za ta koma kudu. Haka dai, haka dai.

Idan an gama da wannan rabon a tsakanin North da South sai kuma a yi wani abu da aka kira Micro Zoning, wato a ware kuma, misali,  sai a ce, a kudun ina? Yarbawa ko Inyamurai ko 'Yan Neja Delta? A arewan 'Yan midil belt, ko mutanen gabas ko Hausa-Fulani? 

Shugaban kasa Muhammad Buhari, a matsayinsa na jagora na APC shi ne kat, don haka aka same shi ya fadi yadda yake so a yi. A bisa bayani sahihi, mukami biyu kawai yake da sha'awar a kyale shi ya fitar. Na daya shugaban jam'iyya na kasa. Anan ya dauki Sanata mai ci kuma tsohon gwamnan jihar Nassarawa, Alhaji Abdullahi Adamu. Shekararsa 75 a duniya kuma tunda aka dawo jamhuriya ta hudu a PDP aka san shi, daga baya ya yi kome zuwa APC. Daya mukamin da PMB ya nemi a bashi, shi ne Mataimakin shugaban jam'iyya na kasa mai lura da yankin Arewa Deputy Chairman North. Anan kuma sai ya bada sunan Faruk Adamu Aliyu. Sauran kujeru kuwa sai yadda gwamnoni suka yi.

A matakin karfin iko da mulki, bayan shugaban kasa, suma gwamnoni a jihohin su sune wuka da nama. Haka APC take, ita ma PDP dabi'arta kenan. Gwamnoni suna da kungiyarsu ta 'yan APC wato Progressive Governors Forum PGF, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu shi ne shugaba. APC tana gwamnoni guda  22, a cikinsu guda 10 suna da burin tazarce, goma sha biyu kuma wa'adinsu ya cika. Sun gama mulki. Wadanda suka fito daga yankin Arewa kowanne daga cikinsu suna son a dauki wanda zai rufawa dan takarar shugabancin kasa daga cikinsu. Kamar kuma gwamna Olukayade Fayemi.na jihar Ekiti yana da sha'awa ko a dauki shi a dan takara, in ba a dauki Bola Ahmed Tinubu ko Farfesa Yemi Osinbajo ba ko daya daga cikin  ministocin Buhari daga Yankin Yarbawa. Duk gwamnonin APC sun rabu gida biyu akan wanda za a marawa baya a batun 2023. Kowa cikinsu yana fafutukar yadda zai dafe wata madafa a maganar zabukan 2023.

A saboda wannan dalilin ne, zaman ranar Lahadi bai kammalu ba, aka sake haduwa a gidan gwamnatin Neja na Asokoro a jiya da daddare. Gwamna  Badaru da takwaransa Bagudu na Kebbi da Fayemi na Ekiti da Abubakar Bello na Neja da ministan shari'a Abubakar Malami suka hadu.

Sun hadu ne akan bukatu biyar. Na farko sake shirya yadda za a yi rabon mukaman jam'iyya a tsakanin yankunan Najeriya biyu. Na biyu, yadda za a tabbatar tsohon dan ACN ko CPC ko ANPP zai karbi ragamar APC na kasa da yankunan Kudu da Arewa na mataimaka. Na uku yadda za a fuskanci wanda arewa za ta bayar a matsayin Mai rufawa dan takarar shugabancin kasa baya. Na hudu, yadda za a samu warware takaddama da sabanin juna akan yadda aka yi shugabancin APC a jihohi. Na karshe kuma shi ne yadda za a takawa Mai Mala Buni burki a kudurin da yake da shi na kin yin kwanbenshin da hade shi guri guda da fidda dan takarar shugabancin kasa.

Wadannan gwamnoni da taimakon hujjoji da dabaru sune suka ja hankalin PMB akan a  ajiye Mai Mala don kuwa zai jawo wa APC matsala. A baya, a cewarsu ya yi kokari, amma daga bisani ya zama hutsu. Bayan sun kammala gamsar da shugaban kasa Muhammad Buhari akan bukatarsu ta a sallami tun a lokacin da yake shirin barin kasar zuwa neman lafiya a Birtaniya, ya lamunce su warware matsalolin yadda suka ga yafi dacewa. Tun da asubahin yau aka fara shirin sauke Mala Buni. Zuwa Azahar har an cika umarnin Baba Buhari. Mai Mala da sunan neman magani a Turai ya tafi, sai bayan kwanbenshin zai dawo ko kuma gab da za a yi.


Comments

Popular posts from this blog

Kano indigene appointed as Chief Vet Officer of Nigeria

FULL LIST: APC inaugurates state chairpersons from 34 state