2023: Jam'iyyar NNPP ce zata lashe manya zabuka - Dr. Kurawa
UMAR IDRIS SHUAIBU - KANO
Guda cikin jiga-jigan jam'iyyar nan ta ' New Nigeria Peoples Party wato (NNPP), Dr. Farouk Kurawa ya bayyana cewa shakka babu jam'iyyar su zata baiwa mara da kunya a babban zabe mai gabatowa na dubu biyu da ashirin da uku.
Dr. Farouk Kurawa na bayyana hakan ne jim kadan da kammala taron jam'iyyar ta NNPC a mazabar Kurawa, dake cikin kwaryar birnin Kano.
Kurawa ya kara da cewa hakan kuwa zai tabbata ne biyo bayan karbuwa da tsagin su na Kwankwasiyya ya samu wajen ciyar da al'umma gaba, karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Idan ba'a manta ba, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana aniyar sa na sauya sheka ne a makwannin da suka gabata, a wani mataki na kama madafun iko a dukkanin matakan mulki dake kasar nan.
Da yake amsa tambaya ko shin sabuwar jam'iyyar zata iya karawa da jam'iyya mai mulki, Dr. Farouk Kurawa yace "duk wanda ya kalli yanayin da ake ciki na kuncin rayuwa da rashin saukin al'amuran yau da kullum da talakawan kasar nan ke ciki, ya san jam'iyya mai mulki ta gaza wajen tafikas da shugabaci, wanda hakan ke alamta faduwar ta a manyan zabuka a shekara mai kamawa ta 2023", a cewar Dr. Kurawa.
Jigo a jam'iyyar ta NNPP, ya kuma bukaci magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya da suyi dukkan mai yiwuwa wajen ganin sun karbi madafun iko, don aiwatar da ayyukan raya.
Comments
Post a Comment