2023: Duk dan kishin kasa ya fito don bada gudunmawa - Tambuwal

Gwamnatin jihar Sokoto tace akwai bukatar duk wani dan kishin kasa ya fito takara a zaben 2023 domin bayar da tasa gudunmawar ceto kasar nan daga mawuyacin halin da take ciki.

Kwamishinan matasa da wasanni na jihar ta Sokoto Comrade Bashir Usman Gorau ne ya bayyana hakan, lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Kano.

Wannan na zuwa ne a wani bangare na taron kaddamar da shugabancin kungiyar matasa masu goyon bayan takarar Gwamna Aminu Tambuwal na jihar ta Sokoto.


Yace Najeriya musamman yankin Arewa na fama da matsalolin tsaro, koma bayan tattalin arziki, tabarbarewar Ilimi da sauransu, wanda bukatar samun jajirtaccen mutumin da zai magance wadannan matsalolin ya zama wajibi.

Taron dai ya gudana ne a cibiyar tunawa da marigayi Malam Aminu Kano dake jihar Kano dake Mumbayya.

Comments

Popular posts from this blog

Sallah: NSCDC deploys 3005 operatives in Kano to ensure safety

How ICRC trains and empower disable, Hisbah guards in Kano

Verify license status of Companies before investing - CBN, SEC advise citizens