Hakimin da yafi dadewa a Kano ya rasu



Umar Idris Shuaibu - Kano

Rahotanni na nuni da cewa Allah ya yiwa tsohon Hakimin karamar hukumar Danbatta rasuwa Alhaji Mukhtar Adnan.

Marigayi Alhaji Mukhtar Adnan ya zama dan majalisar sarki mai nadin sarki tun a shekarar 1954, inda bayan shekaru 9 da samun wannan mukamin a fadar Sarkin Kano ne, suka nada marigayi Dr. Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano a shekara ta 1963.

Marigayi Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan shi ne kwamishinan Ilmi na farko tun a tsohuwar jihar Kano, haka zalika ya taba rike bulaliyar majalisar tarayyar Najeriya.

A lokacin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ne aka sanya sunan marigayin a Kwalejin Kimiyya ta maza dake kan titin State Road wato 'Day Science'.

Comments

Popular posts from this blog

Kano indigene appointed as Chief Vet Officer of Nigeria

FULL LIST: APC inaugurates state chairpersons from 34 state

Rigimar Jam'iyyar APC- Daga Bello Sharada