Gwamnatin Kano zata hana shan shisha a fadin jihar
Umar Idris Shuaibu - Kano
Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin hana ta'ammali da shisha da duk dangogin ta a jihar.
Manajan daraktan hukumar kula da masu yawon bude idanu ta jihar, Alhaji Yusuf Ibrahim Lajawa ne ya bayyana hakan, cikin wata tattaunawa da jaridar Daily News 24.
Alhaji Yusuf Ibrahim Lajawa ya ce hakan na zuwa ne a wani mataki na Gwamnatin wajen ganin ta kara tsaftace jihar Kano daga miyagun halaye da laifuka, da ka iya barazana da tarbiyyar matasa.
Lajawa ya kara da cewa, tun 3 ga watan Nuwambar da ya gabata, Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan dokar hana wadannan laifuka, wanda cikin shekara mai kamawa ta 2022 ne zata fara aiki.
"Dokar ta hada da masu wuraren taruka da ake kira da (event centers) da za su rinka gudanar da harkokin su daga 9 na safiya zuwa 12 na daren kowacce rana, da hana baiwa yara 'yan kasa da shekaru 18 dakuna a otal-otal dake fadin jihar.
Dokar bata tsaya anan ba, ta hada da duk diloli da suke harkar shisha, da masu sayar da ita ko wuraren shanta.
"Tuni hukumar mu ta dauki gabarar nusar da masu wadannan sana'o'i, don ganin basu sabawa wannan doka da zata fara aiki nan ba da dadewa," Yusuf Ibrahim Lajawa.
Manajan daraktan ya kuma da cewa, ya zama wajibi al'ummar jihar Kano su baiwa wannan hukuma hadin kan da ya kamata, wajen ganin tayi nasara kan wannan gagarumin aiki da ta dauko.
Ya kuma yi gargadi cewar wannan doka za tayi aiki ba sani ba sabo da sauran jami'ai don tallafawa hukumar wajen aiwatar da dokar.
Comments
Post a Comment