Ganduje ya naɗa Alaramma Ahmad Sulaiman kwamishina

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Alaramma Ahmad Sulaiman kwamishinan ilimi na biyu a jihar Kano.

Alaramma Ahmad Sulaiman ne ya tabbatar da ba shi wannan muƙamin a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya yi godiya ga Gwamnan.

Ya wallafa hotunansa tare da gwamnan, a gefe akwai Sheikh Abdullahi Balalau wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Izala, da kuma sakataren ƙungiyar na ƙasa Sheikh Kabir Gombe.

Malam Ahmad Sulaiman ya roƙi Allah ya sa albarka a kujerar da ya samu da kuma roƙon addu’ar jama’a kan taya sa riƙo.

Comments

Popular posts from this blog

Sallah: NSCDC deploys 3005 operatives in Kano to ensure safety

How ICRC trains and empower disable, Hisbah guards in Kano

Verify license status of Companies before investing - CBN, SEC advise citizens