Dan Sarauniya ya shawarci Gwamna Ganduje ya koma makarantar allo
Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Injiniya Mu'azu Magaji Dan Sarauniya ya shawarci Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya koma makarantar allo domin koyar yadda ake tafiyar da al’umma, tare da sanin matsayin iyali a sha'anin tafiyar da mulki.
Dan Sarauniya ya wallafa hakan ne a shafin sa na Facebook, dai-dai lokacin da Gwamna Ganduje ya tafi kasar Amurka domin daukar kwas kan yadda ake gudanar da mulki a jami’ar Harvard.
Dan Sarauniyar cikin rubutun da ya wallafa ya ce a wannan lokaci Gwamna Ganduje baya bukatar karin wani ilimi daga Jami’ar Havard, don kuwa karatun da ya samu daga jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria da jami’ar Ibadan sun ishe shi, abinda yake bukata bai wuce ilimin da ya rasa tun a baya wato ilimin makarantar allo
A cewar Injiniya Mu'azu Magaji ta haka ne Ganduje zai gane yadda ake tafiyar da dukiyar al’ummar da ake shugabanta da kuma amfanin nada mataimaka wanda zasu taimaka masa wajen gudanar da harkokin mulkin al'umma.
Cikin watan Afrilun shekarar da ta gabata ne Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sauke Injiniya Mu'azu Magaji daga mukamin kwamishinan ayyuka biyo bayan wasu kalamai da yayi wanda ke nuna cewa na murna da rasuwar tsohon shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari ne.
Ganduje ya sake nada Dan Sarauniya a matsayin shugaban kwamitin aikin janyo bututun gas daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano, inda a nan ma Ganduje ya sauke shi a baya-bayan nan.
Bashida hali shiyasa
ReplyDelete